DA ƊUM!-ƊUM!: Dr. Bala Wunti Ya Saya Wa Wasu Bayin Allah Gida Bayan Korarsu Daga Gidan Haya a Jihar Bauchi
A ci gaba da nuna halin jin kai da t@imakon al’umma, Dr. Bala Wunti ya tallafa wa wasu bayin Allah da aka kore su daga gidan haya cikin dare, inda ya saya musu sabon gida don su samu mafaka mai dorewa.
Baya ga hakan, Dr. Wunti ya bayar da umarni na musamman da a sanya yaran wadanda abin ya shafa a makarantar Islamiyya da kuma boko, domin cigaba da samun ingantaccen ilimi da tarbiyya.
Wannan aikin alheri na Dr. Wunti ya ja hankalin al’umma tare da bayyana shi a matsayin gwarzon da ke rayuwa cikin mutane, yana ciyar da su gaba da taimako mai ma’ana.
@Dokin Karfe TV