INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN 😭
Ashe tun bayan kîsan Dan Ta'ådda (Halilu Sububu) da sati biyu (2) aka kameshi aka tsareshi A cikin wata 'Barrack' dake Gusau kafin daga bisani ayi gaba dashi zuwa Abuja 😭.
Yanzu dai munada tabbacin wannan bawan Allah yana nan tsare kuma a Abuja sannan ko danginsa ba'a taɓa bari sunyi magana dashi ba Ballai susan halinda yake ciki.
Jama'a wallahi haƙin mune muyi kiranye tako wace hanya domin yasami yanci daga halinda yake ciki, idan kuma mukayi shiru bamu nuna damuwa ba, to lallai bamu yimasa adalci ba domin saboda murayu cikin salama yashiga wannan halin.😭
Allah ya kawo masa mafita ta alkhairi AMEEN THUMMA AMEEN.
********""********👇
Jarumi a cikin jarumai
Bayanai sun bayyana cewa wannan sojan shi ne wanda ya kashe ƙasurgumin ɗan bindigan nan Halilu Sububu, da wasu gaggan yaran ɗan bindigan. Waɗanda su ka addabi al'ummar jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa.
An tabbatar da jarumi ne na yankan shakku, domin ance harda hannu yake kama ƴan bindiga.
Wani fata ku ke mishi?
Daga 👉Comrade Zakari Ya'u Adamu, Kantagora