Yadda Aka gudanar da taron addu'o'i ga tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari a taron majalisar zartaswa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ne ya jagoranci taron addu'o'in kuma taron ya samu halarcin iyalan marigayin da ministoci da sauran manyan ‘yan siyasa a Najeriya.