DÆN D@BAN DA YA JAWO AKA K@SHE DPO NA RANO
Wannan shine dan dæban da ya jawo aka k@she DPO, Sunan yaron Abdullahi Musa, r!kakkën dan kwæya ne kuma dan dæba, ana masa lakabi da sunan "Kuli" sunan anguwarsu Gada anan cikin garin Rano jihar Kano,
Bayan kasancewarsa dan kwæya kuma dan d@ba masu kwacen waya, yaron yana da wata dabi'a, yana cire salansan mashin yayi ta zuga gudu a cikin anguwanni shi da abokansa suna tæda hankalin al'ummah suyi ta bugë yaran mutane...
Duk wanda yake cikin garin Rano musamman anguwar da yaron yake ya san cewa wannan dabi'arsa ce, ya addabi kowa, baya ganin mutuncin kowa, an sha kama yaron daga bisani a bada belinsa, ga hotonsa nan ya isheku izna ga dabi'arsa
Musabbabin mutuwar yaron a hannun 'yan sanda shine; ana saura kwana biyu ya mutu, ya cire salansa ya bi wata anguwa sai aka tareshi har aka samu wani ya wankeshi da mari, sai yaron yaje ya kwaso abokansa 'yan daba akan zai je gidan wanda ya mareshi su kashe shi
Shine mutumin da yayi marin ya ki komawa gida, ya kai kara gurin 'yan sanda, bayan ya samu labari 'yan sanda na nemansa sai ya gudu, amma daga bisani an kamashi, kuma an dakeshi wanda hakan ne yayi sanadin mutuwarsa
Bayan mutuwar dan daban, sai kaninsa shima dan daba ne ya je ya kwaso abokansa 'yan daba suka je suka kone police station na Rano, suka lalata motoci, suka kai ga DPO suka kashe shi kisan wulakanci
Sanan mutumin da ya kai karan dan daban, sun sake komawa gidansa zasu kashe shi basu sameshi ba ya gudu tare da iyalansa, sai suka kone gidansa da gidan makwabcinsa, komai a gidan ya kone kurmus, wannan shine abinda ya faru, kowa yaje ya bincika
Irin wadannan yara batagari an san su, amma mutanen gari basa taimaka wa domin a hukuntasu ta hanyar shari'ah, sai idan jami'an tsaro sun wuce gona da iri wajen hukuntasu azo ana kunfar baki, mutanen Kano sun san illar 'yan daba, babu amfanin a bawa dan daba mafaka ko kadan
DPO na Rano CSP Aliyu Muhammad yayi jarunta, ya sadaukar da rayuwarsa domin ya takaita asaran rayuka, muna fata Gwamnatin Maigirma Gwamnan jihar Kano "Engr Abba Kabir Yusuf" zata karrama iyalansa ta hanyar kyautata musu
Muna rokon Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljannah ne makomarsa













