Yan Bînd!ga Da Dama Sun Miƙa Wuya Tare Da Ajiye Makamansu Bayan Gumurzu Da Sojoji, ida suka bukaci ayi Sulhu A Jihar Katsina.

Dä DUMIDUMINSA: 'Yan Bînd!ga Da Dama Sun Miƙa Wuya Tare Da Ajiye Makamansu Bayan Gumurzu Da Sojoji, ida suka bukaci ayi Sulhu A Jihar Katsina.

Daga Comr Nura Siniya 

Wasu shuwagabannin ‘yan bindigà waɗanda suka addabi yankin Batsari, Safana da Jibia a jihar Katsina, sun miƙa wuya tare da aje makamansu bayan gumurzu da sojoji, domin rungumar zaman lafiya.

Katsina Reporters ta samu cewa, shuwagabannin 'yan bin-digar da suka miƙa wuya, sun hada da ƙasurgumin dan fashin daji, Abu Radda, Umar Black da Abdullahi Lanƙai, Jijjige da kuma dabar Musa Ɗan gandu daga yankin garin Jibia a Katsina.

A cikin jawaban tubabbun 'yan bindigar sun nemi gwamnati ta duba bukatunsu wajen gina masu kasuwanni da asibitoci da kuma samar musu da ruwan sha, domin yin rayuwa mai inganci.

A yayin zaman kungiyar mutanen yankin da matsalar tsaro ta shafa, (NCSOSACK) karkashin jagorancin Comrd Hamisa S Batsari, sune suka wakilci al'ummar da matsalar tsaron ta shafa a yankunan.

A karshe, shuwagabannin ‘yan bin-digar sun miƙa makamansu ga sojojin, inda suka sako wasu mutanen da suka yi garkuwa da su tare da ɗaukar alkawarin rungumar zaman lafiya.

Me zaku ce?


Ku Kalli Cikakken Bidiyon 🎦 👇 













Ku Kalli Cikakken Bidiyon 🎦 👇 

Related Post

LABARINA Season 11 Episode 13










👇👇


Post a Comment

Previous Post Next Post