Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'unðŸ˜
Allah Ya yi wa matar fitaccen daɗaɗɗen jarumin Kannywood, Ibrahim Maishunku Rasuwa a ranar Laraba, 23 ga watan Oktobar 2024 sakamakon ciwon Ƙoda.
Amina Abdoul, wadda iyayen ta su ka fito daga kasashen Sudan da Senegal, ta zaune a yankin Brooklyn na birnin New York ta Ƙasar Amurka ta kasance ita ce mata ta biyu ga jarumi Maishunku, wadda su ka yi aure a shekarar 2018, kimanin shekaru 6 da su ka gabata kenan.
Kamar yadda jarumi Maishunku ya bayyana, sun fara haɗuwa da Amina ne a shekarar 2007 a matsayin mai kaunar fina-finan sa wato FAN. Daga nan alaƙar ta cigaba har zuwa shekarar 2018 lokacin da su ka yanke shawarar zama ma'aurata, kuma aka ɗaura bisa tsarin Addinin musulunci.
Kuma ita ce ta kasance matar sa tun bayan rabuwar shi da matar sa ta farko har zuwa lokacin da Allah Ya karɓi rayuwar ta.
Maishunku ya kadu sosai da rasuwar matar sa Amina, wadda ya bayyana a matsayin mace ɗaya tamkar da dubu ta fuskar hankali da sanin ya kamata da ba su taɓa samun wani saɓani a tsakanin su ba.
Amina dai ta rasu ne a wani Asibiti a can ƙasar Amurka dalilin tsanantar da ciwon Ƙodar da ta shafe tsawon lokaci ta na fama da shi. An dai yi mata sutura kamar yadda Addinin musulunci ya tanada.
Da fatan Allah Ya jiƙan ta da rahamarSa, Ya bawa iyalai, ƴan uwa da abokan arziki hakurin rashin ta. Amin.🤲
- Ahmad Nagudu
- Nagudu TV 📺
Allah yaji kanta da Rahama 🤲
RELATED POST 👇





