Da Dumí-Dumí: Ni ba masifaffiya ba ce, shirin fim ne kawai - In ji Baba Lami ta cikin shirin Fim din Garwashi.👌
Fitacciyar tauraruwar fina-finan Hausa, wadda yanzu take fitowa a matsayin Baba Lami a shirin Garwashi, ta ce mutane da dama suna yi mata fatan mutuwa saboda rawar da take takawa a matsayin masifaffiya kuma muguwa.
A hirar da ta yi da TRT Afrika Hausa, Mama Balaraba Abdullahi, wanda shi ne sunanta na gaskiya, ta ce a zahiri ita ba masifaffiya ba ce.






