A Jiya Al-Hamis An Fara Raba Abincin Da Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Ya Ɗauki Nauyin A Raba A Cibiyoyi 12 A Birnin Maiduguri Na Jihar Borno...

A Jiya Al-Hamis An Fara Raba Abincin Da Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Ya Ɗauki Nauyin A Raba A Cibiyoyi 12 A Birnin Maiduguri Na Jihar Borno 

Jarumar Kannywood, kana kuma ta hannun daman Rarara, A'isha Humaira tana cigaba da jagorantar aikin dafa wa gami da raba abinci ga al'ummar birnin Maiduguri ta jihar Borno waɗanda iftila'in ambaliyar ruwan sama ta ɗaiɗaita.

A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, an ware cibiyoyi (wuraren dafa abinci) kimanin guda 12 a wurare daban-daban da ke faɗin birnin Maiduguri.

A jiya Alhamis rana ta farko ta fara aikin, kowace cibiya ɗaya an dafa babban buhun shinkafa guda daya da taliya makaroni katan 14 da kuma buhun Fulawa biyu wanda ake yi fanke aka yi karin kumullo da su.

Baya da haka, kowane buhun shinkafa guda ɗaya da aka dafa ya ciyar da aƙalla mutum 250. Ɗumbin al'umma ne suka amfana da wannan tallafi.

Idan ba ku manta ba, A'isha Humaira ta kai agajin gaggawa birnin Maiduguri ta raba Bargunan ruhuwa, kayayyakin sa wa, magunguna, da kuma agajin abinci na gaggawa irin su biredi domin kare al'umma daga faɗawa cikin yunwa bayan faruwar wannan iftila'i na ambaliya.

Ganin haka ne kuma ya sanya Rarara ya nemi da ta huta ya tura mata kuɗaɗe domin ta gudanar da aikin ciyar da al'ummar kamar yadda ta bayyana hakan a shafinta tare da yi masa godiya a madadin al'ummar Jihar Borno.

Daga Dokin Karke TV✍️








Ku Kalli Cikakken Bidiyon 🎦 👇 


Post a Comment

Previous Post Next Post