YANZU -YANZU;
Rarara Ya Ɗauki Nauyin Auren Mutane 8 Zai Aurar Da Su A Gobe Juma’a
Fitaccen mawaƙi, Dauda Kahutu Rarara zai aurar da mutane 8 waɗanda shi ne ya ɗauki nauyin auren gaba ɗaya, shi ne uwa, shi ne kuma uba na angwaye da amaren gaba ɗaya, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta samu rahoto.
Daga ciki akwai ƴaƴan abokinsa da ya rasu, mawaƙi Isyaku Forest su biyu waɗanda zai aurar da su ga yaransa, abokan aikinsa.
Daga cikin waɗanda za a aurar ɗin tuni aka ɗaura auren 1. Sulaiman Hassan (Andos) mai kiɗa da amaryarsa, Zainab Sani Babyn Coffee, makonni biyu baya.
Ga jerin sunayen sauran angwaye da amaren kamar haka:
2. Ahmad Idris (Delta) Mawaƙi,
Da amaryarsa,Habiba Ishaq Forest
3. Habibu Sa’idu Muhd
Da amaryarsa, Fatima Ishaq Forest
(Hoton su habibu bai zama ready ba ,zaku gansu a event In Shaa Allah )
4. Abdullahi Ibrahim (Abbany Rarara)
Da amaryarsa Hamida Haladu Adam.
Za a ɗaura auren a gobe idan Allah ya kaimu bayan Sallar Juma’a, a Masallacin Murtala Hausawa da misalin ƙarfe 2 na rana.
Ana gayyatar kowa da kowa.
Dokin Karfe TV ✍️
Related Post
Da Ɗum!Ɗum!nsa:
Motata Za Ta Iya Sayen Wasu Motocin Alfarma Har Sau Uku, Idan Ba A Yarda Ba A Tambayi Sarkin Mota, Inji Naziru Sarkin Waƙa,Naziri wanda ya furta hakan a wani bidiyonsa, ana zargin kamar yana mayar da martani ne ga Rarara wanda kuma ya yi hakan ne domin kare mutuncin wani masoyinsa.
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Rariya ✍️