Ka Da Ƙiyayyar Shugaba Tinubu Ta Sa Ku Goyi Bayan Mutanen Da Suka Lalata Ƙasarku Najeriya
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Duba da irin mutanen da suka haɗu suke neman dunƙulewa waje ɗaya domin su karɓi mulki a 2027, ya kamata ƴan Najeriya su yi wa kansu karatun ta nutsu su gane cewa waɗannan mutane sune dai mutanen da suka ba wa amana a baya amma suka lalata musu ƙasa.
Sannan, idan muka sake duba mutanen, wasu daga cikin mutane ne da suka samu dama a gwamnatin baya ta Buhari, shin me suka yi muku ? Kun ga kenan sun fito wannan yaƙi ne saboda shugaban ƙasa Tinubu bai ba su dama ba domin kuwa wasu daga cikinsu ma har wajen rantsuwa sun halarta amma saboda yadda suka ga ana wannan gwamnati babu su shi isa suka fito domin su ɓarar kowa ya rasa, ba wai talaka ne a gabansu ba.
Dan haka, ya kamata mu zama wayayyu, mu riƙa amfani da wayewarmu da tunaninmu muna auna abubuwa da idon basira. Wannan mutanen duk abu ɗaya ne. Wasu za su yi amfani da wani hali da ake ciki su nemi goyon bayan talaka wanda kuma ba za su taɓa so matsalar ta ƙare ba. Idan aka duba tarihi ma su ne suka jefa ƙasar a halin da take ciki na rashin tsaro da tsadar rayuwa yanzu kuma suke son a ƙara ba su dama su ƙara rusa ta.
Ya kamata mu kula sosai, kar mu zama ƴan bin kururuwa da makancewa a kan dole sai abu kaza wanda ƙila kuma ba shi ne alkhairi a gare mu ba. A shekarun baya mun ce lallai dole sai Buhari, shin da Buharin ya zo daɗi muka ji ko wahala muka sha ?
Dokin Karfe TV ✍️
Related Post
Maryam Waziri (Laila Labarina) ta samu Lafiya bayan hatsàrin motar da sukayi, wanda har Ɗansu ya "Ràsu" da kuma Ɗan'uwan Mijinta...
Ku kalli Bidiyon 👇
Labarina Season 11 Episode 7
















