RARARA YA B@WA TIKTOKERS 2O,000,000.00
Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji "Dauda Kahutu Rarara" Ya Ware Naira Miliyan Ashirin 20,000,000.00 Ya Bawa Masoyansa Tiktokers Masu Hawa Wakokinsa a Tiktok Domin Suma Suje Suyi Bikin Babbar Sallah Cikin Nishadi.
Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara Yace Soyayya Ce Tasa Suke Hawa Wakokinsa Domin Akwai Wadanda Idan Aka Shiga Profile Dinsu Na Tiktok Za'aga Duk Wakokinsa Suke Sakawa, Wasu Sun Taba Ganinsa Azahiri Wasu Kuma Basu Taba Ganinsa ba, Kawai Kauna Da Soyayya Ce Tasa Babu Dare Babu Rana Kullum Hawa Wakokinsa Sukeyi a Tiktok Shiyasa Shima Yace Bari Ya Saka Soyayya Da Soyayya Yace Ga Miliyan 20,000,000.00 Ashirin Domin Suje Su Siyi Ragunan Sallah.
Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara Ya Bada Naira Miliyan Ashirin Din Ne 20,000,000.00 Ta Hannun Amininsa Kuma Amintaccansa 'Dakta Abdullahi Al Hikimah' Daga Karshe Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara Yayi Musu Godiya Da Fatan Allah Yasa Ayi Bikin Babbar Sallah Lafiya.
Rabi'u Garba Gaya
Media Aide To Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara.