Mahaifin jarumar Hausa film Rahama Sadau ya rasu a yau, kuma har anyi jana'izarsa

 MUTUWA WA'AZI NE

Mahaifin jarumar Hausa film Rahama Sadau ya rasu a yau, kuma har anyi jana'izarsa

Muna amfani da wannan dama wajen isar da sakon ta'aziyyah da nasiha ta 'yan uwantaka zuwa ga jaruma Rahama Sadau 

Muna miki ta'aziyyah Allah Ya jikan Mahafinki, Allah Ya sa dan Aljannah ne, Allah Ya gafarta masa tare da dukkan 'yan uwa Musulmi da suka rigamu gidan gaskiya 

A babi na nasiha zuwa gareki wannan mutuwa da aka miki ta isheki wa'azi, babu wani nasiha da za'a miki fiye da wannan

Rahama Sadau ki sani cewa hanyar da kike kanta ba hanya bace mai kyau da zata sa ki hadu da Allah lafiya, lokaci bai kure miki ba da zaki tuba ki gyara, ki watsar da harkan film da yawon duniya, kiyi aure ki rufa wa kanki asiri domin ki hadu da Allah Mahaliccinmu lafiya

Bani da wata hanya da zan isar miki da sakon ta'aziyyah da nasiha sai ta nan, idan nasihar tayi zafi kiyi hakuri

Allah Ya jikan dukkan Musulmi, Ya bamu ikon gamawa da duniya lafiya muna Musulmai masu imani

Datti Assalafiy ✍️ 



Related Post 

Yadda Aka yi wa wasu matafiya ɗaurin aure 12 daga Zariya k!san g!lla, sai mutum 11 yara, Maza da Mata na kwance a asibiti bayan wasu mutane sun kai musu hari a yankin karamar Hukumar Mangu dake Jihar Filato

Ku kalli Bidiyon 









Related Post 

Fuskokin Wasu Fitattun Jarumai Da Suka Halarci Taron Shagalin Bikin Jarumi Kuma MC Ibrahim Sharukhan, Wanda akafi sani da (MC na Manzon Allah) A Birnin Kano...


Ku kalli Bidiyon 👇 












Post a Comment

Previous Post Next Post