DA DUMI-DUMI: Mawaki Rarara Zai Auri Yarinyarsa Jaruma A'isha Humaira.
Shahararren mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara na shirin auren jarumar Kannywood, Aisha Humaira.
Kamar yadda wata majiya ta kusa da Angon ta zanta da Kano Times da ya nemi a sakaya sunansa, ta ce za a daura auren ne a gobe Juma’a a birnin Maiduguri na jihar Borno, da zarar an kammala sallar Juma’a.
Majiyar ta bayyana cewa, "An shirya komai, za a daura auren ne a Maiduguri bayan sallar Juma'a.
Rarara ya yi aiki tare da Aisha Humaira tsawon shekaru. Dangantakar su, a cewar wasu ta yi girma a cikin sana'a da kuma na sirri.
An dade ana Yaɗa jita jitar cewa akwai alaƙar soyayya tsakanin mawakin da Jarumai A'isha Humiara kasancewar Alaƙarsu ta kusa a bayyane.








