Na Ɗauki Fim A Matsayin Sana’a, Iyayena Sun Ba Ni Tarbiyyar Da Ba zan Aikata Abinda Zan Janyo Musu Zagi Ba...


Na Ɗauki Fim A Matsayin Sana’a Iyayena Sun Ba Ni Tarbiyyar Da Ba zan Aikata Abin Da Zan Janyo Musu Zagi Ba, Cewar Ayeesha Soba

Jaruma mai tasowa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, A’isha Abubakar Soba ta bayyana cewa babban burinta a yanzu shi ne ta samu ɗaukaka Duniya ta san ta har ma ta yi alfahari da ita.

Soba wacce ta bayyana hakan ta cikin tattaunawarta da Jaridar Dokin Ƙarfe TV, ta kuma ƙara da cewa, ba ta fuskanci wani ƙalubale ba tun bayan shigarta harkar Fim, kamar yadda ta ce: "Ina son harkar kuma na faɗo hannun nagari. Kowace sana’a akwai nagari akwai saɓaninsu, kuma in ka kame mutuncinka ba abin da zai same ka". Inji ta.

Ta kuma ci gaba da cewa "Idan kina jaruma ki sani cewa wata rana za ki bar Fim ki yi aure, dan haka kar ki aikata abin da in an tuna ki za a yi tir da ke, ki aikata abin da ko da bayan ba kya nan za a tuna da ke a ce son barka tayadda in an ga wasu suna aikata ba daidai ba za a ce ai ku ba haka kuka yi ba".

Daga nan ta ƙara da cewa: "Ni na ɗauki fim ne a matsayin sana’a, kuma na samu iyayen gida da ke ɗora ni a kan hanyar yin abin da ya dace. Ba zan taɓa ba su kunya ba, kuma ba zan taɓa yin abin da zan jawo wa iyayena abin kunya ba domin sun ba ni tarbiyya". In ji ta.

A’isha Soba, ta kuma ƙarƙare da cewa a shirye take ta yi aure nan gaba idan miji ya fito, kuma tana da burin aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda ke ayyukan wayar da kai da kare mutuncin mata da tallafawa mata da yara ƙanana.

Wanne fata zakuyi mata?








Related Post

LABARINA Season 11 Episode 13










👇👇


Post a Comment

Previous Post Next Post