Dazu-Dazu: Mai Girma kwamishiniyar Kidaya ta Kasa Hajia Saa Dogon-bauchi ta Sadaukar da Lambar Yabo da aka bata a Jahar Kaduna na karrama Jajirtattun Mata Ashirin ga Hussaina Iliyasu (Matar Abbas Soja).


Dazu-Dazu: Mai Girma kwamishiniyar Kidaya ta Kasa Hajia Saa Dogon-bauchi ta Sadaukar da Lambar Yabo da aka bata a Jahar Kaduna na karrama Jajirtattun Mata Ashirin ga Hussaina Iliyasu (Matar Abbas Soja).


Kwamishiniyar ta bayyana haka ne ta wayar salula inda tace irin su Hussaina ita ya kamata a karrama domin kuwa irinsu ake kira Jarumai, a cewar Kwamishiniyar Samun irin su Hussaina a wannan lokaci Rahama ne, domin kuwa ta tabbatar da duniya har yanzu akwai Mata masu Juriya da Tausayi, Amana da Jajircewa a cikin al’umma

KU Kalli Cikakken Bidiyon 🎦 👇 


Kwamishiniyar wacce a halin yanzu bata Nigeria, ta nemi duk wanda yake da number Matar Soja ya aike Mata da shi.

Inda ta bayyana Kaduwar ta game da lamarin tare da nuna tsantsar tausayi da tashin hankali da abinda ya faru ga Hussaina da Abbas.

Ta kuma sha Alwashin bibiyar lamarin, domin kwatowa Sea Man Abbas da Matarsa Yanci. Inda a halin yanzu ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da Adalci.

A karshe Babbar Kwamishiniyar tana aikewa Al’umman Musulmai Barka da Zagayowar watan Maulidi.

~Salma Musa

SA Media arewa women for Tinubu-Shettima/ubasani

@Dokin Karfe TV✍️










Allah ya bimusu hakkin su 🤲 

Post a Comment

Previous Post Next Post